Rundunar Ta bayyana zargin da kungiyar kare hakkin ta duniya ta yi a matsayin ƙeta haddi kuma abin mamaki wanda bashi da tushe balle makama.
Sannan ta kara da cewa sojojin Najeriya na da ƙwarewa da bai kamata kungiyar tai mata irin wannan zargin ba.
Sannan Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar a wani taron manema labarai ne da ya gudana a Maiduguri a ranar Alhamis ta zargi sojoji da birne wasu fararen hula 10,000 cikin kabari bayan mutuwarsu a lokacin da suke tsare a hanunsu.
Sai dai daraktan yada labarai na rundunar tsaron ƙasar, Edward Buba, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa ba za su so shiga wasu al’amura da kungiyar ba, saboda ana bin ka’idojin aiki wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi kama fararen hula.
Buba, ya ce rundunar ta yanke shawarar gayyatar kungiyar ce domin ta kawo hujjojin da za su tabbatar da bayanin da ta yi, domin baiwa sojoji damar gudanar da bincike saboda a gano sahihancinsa ko akasin haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI