Kwamishinan ƴan sandan jihar Mohammed Dalijan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ƴan bindigar sun yi wa jami’an tsaron kwantan ɓauna ne a lokacin da suka yi yunkurin kai ɗauki wurin da ƴan bindigar suka kai hari.
Sai dai ƙwamishinan ƴan sandan ya tabbatar da cewar jami’an tsaron sun yi kokarin daƙile harin da ƴan bindiga suka kai kamfanin gine-ginen na Setraco.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Ƴandoto da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe na jihar Zamfara, da misalin ƙarfe 9 na safiyar jiya Alhamis.
Jaridar Daily Trust da ake walfawa a Najeriya, ta ruwaito cewa harin shi ne na biyu da ƴan bindigar suka kai kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau` cikin ƴan sa’oi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama da ke amfani da hanyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI