Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi a Abuja.
Mr Gabkwet ya ce rundunar musamman ta Operation Whirl Punch ta ci gaba da aikinta na gano sansanin ƴan ta’addda tare da tarwatsa su.
Ya ce bayanan sirri sun bayyana cewa ƴan ta’addan da ke addabar al’umma ta wajen kisa daa yin garkuwa da su a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja su na zaune ne a jihar Kaduna.
A cewarsa, karin bayanan sirri sun nuna cewa waɗannan ƴan ta’adda su na ƙaura daga dajin Allawa na jihar Neja zuwa dajin Malum na ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
A yankin Neja Delta kuwa, Gabkwet ya ce dakarun saman ƙasar a ƙarƙashin rundunar musamman ta Operation Delta Safe sun lalata matatun ɗanyen mai da aka yi ba bisa ƙa’ida ba har guda 25 a yankin Ohaji/Egbema
Na jihar Imo da Degema na da Cawthorne Channel a jihar Rivers.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI