A jawabin da ya gabatar gaban manema labarai jiya Alhamis a Abuja game da nasarorin da rundunar ta samu a wannan shekara, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Sojin Najeriyar Edward Buba ya ce daga watan Janairun shekarar nan zuwa Disamban da muke, rundunar ta kuma kame mutanen da ake kyautata zaton ƴan ta’adda ne waɗanda yawansu ya kai dubu 11 da 623.
Jami’in ya kuma bayyana yadda dakarun Sojin na Najeriyar suka tseratar da mutanen da yawansu ya kai dubu 6 da 376 daga hannun masu garkuwa da mutane.
A cewar Edward Buba tun daga farkon shekarar nan dakarun rundunar Sojin Najeriya ke fama da barazanar ƴan ta’adda daga yankuna biyar na ƙasar wanda ya sanya su matsa ƙaimi wajen ganin sun daƙile duk wata barazana don baiwa ƙasa kariya.
Yayin mabanbantan sumamen da rundunar Sojin ta kai a wurare daban-daban da ke fuskantar barazanar tsaro, Buba ya ce dakarun Najeriyar sun yi nasarar ƙwace tarin makamai da suka ƙunshi bindigogi dubu 8 da 216 baya ga alburusai subu 211 da 459 waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 57.
Sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da ganin barazanar tsaro ko da ya ke yankunan da suka fi ɗaukar hankali bai wuce arewa maso yammcin ƙasar da kuma arewa maso gabashi ba, sai kuma yankin kudu maso gabashi.
A shekarar da muke ciki ta 2024 an ga yadda matsaloli masu alaƙa da Boko Haram ke ƙokarin dawowa ƙari kan ƴan bindigar da tuni suka dagula lamurran ƙasar a wani yanayi da aka ga ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta'addanci da ake kira Lakurawa yayinda a gefe guda IPOB ke ci gaba da cin karenta babu babbaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI