Sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙƙun ƴanbindiga 2 a jihar Zamfara

Sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙƙun ƴanbindiga 2 a jihar Zamfara

Janar Christopher Musa ya ce dukkanin mutanen biyu ƴanbindiga ne da rundunar Sojin Najeriyar ke nema ruwa a jallo saboda ta’addancin da suka shafe lokaci suna yiwa jama’ar jihar ta Zamfara harma da jami’an tsaro.

Janar Musa dake wannan batu yayin bikin kulle wani taron kwamandojin rundunonin ƙawancen tsaro daya gudana a shalkwatar tsaron Najeriyar dake Abuja, yace anyi nasarar hallaka riƙaƙƙun ƴan bindigar ne a sumamen rundunar ‘Operation Show No Mercy’ daya gudana a garin Ruwan Dawa na ƙaramar hukumar Maru a jihar ta Zamfara.

A cewar Janar Christopher Musa dakarun Sojin na Najeriya sun tattaru a sansaninsu na Hannu Tara wanda ke gab da babbar hanyar Magami zuwa Ɗan Sadau, kuma anan ne suka gudanar da aikin nasu bisa tallafin mayaƙan sakai.

Shugaban Sojojin na Najeriya ya ce baya ga riƙaƙƙun ƴanbindigar 2 akwai kuma manyan Sojojinsu 4  da dakarun suka hallaka a wannan aiki, wanda akayi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Bayanai sunce Sojojin na Najeriya sun yi nasarar kakkaɓe manyan ƴan bindiga 6 dake addabar al’ummar ta jihar Zamfara inda suka kuma ƙwace tarin makamai da babura guda 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)