Shugaban Najeriya ya karbi rahoton kwamitin kafa ma'aikatar kula da lamuran dabbobi

Shugaban Najeriya ya karbi rahoton kwamitin kafa ma'aikatar kula da lamuran dabbobi

Mai magana da yawun shugaban kasar ne bayo Onanuga ya ba da wannan sanarwa a shafinsa na X wadda aka fi sani da twitter.

Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, ya karbi rahoton kwamitin fadar shugaban kasa kan aiwatar da sauye-sauyen kiwon dabbobi daga hannun mataimakin shugaban kwamitin Farfesa Attahiru Jega a fadar sa dake babban birnin kasar Abuja, ranar Alhamis 19-09-2024.

Shugaba Tinubun ne ke shugabantar kwamitin amma tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ne Attahiru Jega, ke jagorantar dukkanin kaikomon da ya gudana.

Wani bangare na aikin kwamitin shine samar da hanyoyin kafa ma'aikatar kula da dabbobi.

A yayin da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta ruwaito sanarwar da shugaban ya fitar na shirin samar da ma’aikatar domin magance matsaloli da sukayi katutu a bangaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)