Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fara ziyarar aiki a Najeriya

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fara ziyarar aiki a Najeriya

Steinmeier ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe inda ministan birnin tarayyar Abuja Nyesom Wike ya tarbeshi.

A ziyarar da shugaban na Jamus Steinmeier ya kai Najeriya zai tattauna da shugaban ƙasar Bola Tinubu da kuma shugaban Kungiyar Tatttalin Arzikin Ƙasashen Afika ta Yamma ECOWAS Alieu Omar Touray.

Shugaban na Jamus zai kuma je birnin Lagos domin tattaunawa da wakilan ƴan kasuwa da wakilai a fannin al’adun ƙasar da kuma kungiyoyin fararen hula da tattaunawa da Dr Nike Okundaye da Prof Wole Soyinka.

Ana ganin shugaban na Jamus Frank-Walter Steinmeier zai samu damar zagayawa a birnin Lagos domin ganin irin ci gaban da aka samu da ma ƙalubalan da muhalli ke fuskanta da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)