Yakubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Rotimi Oyekanmi, babban sakataren yada labaran sa ya sanya wa hannu a madadin sa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani dandali na yanar gizo da wasu kafafen sada zumunta sun yi ta yaɗa labarun cewa shugaban INEC ya rasu a wani asibiti da ba a bayyana ba a Landan, bayan rashin lafiya.
Amma da yake mayar da martani, a cikin sanarwar, Yakubu ya ce an ja hankalinsu ne game da labarin karya da wani sashe na kafafen sada zumunta ya yada cewa wai shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya rasu a wani asibitin Landan. Labarin dai ya fara fitowa ne a ranar Litinin, 9 ga Disamba, 2024.
Shugaban bya ci gaba da cewa wannan zancen ƙanzon kurege ne tun da dai gashi yana raye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI