Shugaban Ghana ya ce tsaro ya taɓarɓare a Sahel tun bayan fitar dakarun Faransa

Shugaban Ghana ya ce tsaro ya taɓarɓare a Sahel tun bayan fitar dakarun Faransa

 Akufo-Addo, wanda a bayyana haka a wata ganawa da ya yi da tashar talabijin ta France 24, ya ce shawarar waɗannan ƙasashe na yankin Sahel ta ficewa daga ƙungiyar wani koma-baya ne, yana mai jaddada mahimmancin sake dawowa cikin kungiyar, inda ya ce matsalar tsaro ta ta’azzara a ƙasashen tun bayan janyewar dakarun Faransa daga yankin na Sahel a shekarar da ta gabata.

Shugaban na Ghana ya ce ya fito fili ƙarara cewa sojojin da ke mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar ba su da niyyar sauka daga kan karagar mulki, ballantana su yi maganar zaɓe.

Ɗangantaka ta daɗa yin tsami tsakanin Ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yammacin nahiyar Afrika da jagororin gwamnatin mulkin sojin waɗannan ƙasashe 3 ne tun bayan da sojojin Nijar ƙarƙashin jagorancin Abdourahmane Tchiani su ka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)