Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin ta ƙaddamar da sabon jirgin shugaban ƙasa kirar Airbus A330, ba tare da bayanin yadda aka sami kuɗin sayen jirgin ko kuma sahalewar majalisa ba.
An dai fara cecekuce kan sayan jirgin ne bayan wanda aka saya tun zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya fara bada matsala a tafiye-tafiyen da aka yi da shi zuwa ƙasashen Saudiyya, Netherlands da kuma Afrika ta Kudu.
Wasu bayanan sirri daga fadar shugaban na cewa an sayi sabbin jiragen ne kawai saboda wanda shugaban ke hawa ya shafe shekaru 19 ana amfani da shi.
Sai dai wani sabon bincike ya nuna yadda shugaban Amurka ke amfani da jirgin saman da ya shafe shekaru 34 ana amfani da shi, iyaka a kai shi wajen gyara da sauran su.
Fadar shugaban Najeriya ta sha nanata cewa lalacewar jirgin da shugaban kasa ke amfani da shi abin kunya ne kuma bai dace a ce ana ci gaba da amfani da shi ba.
To amma abinda ya fi ɗaurewa jama’a kai shine yadda aka sayi jiragen da kuma inda aka samo kudaden, dai-dai lokacin da ƴan ƙasar ke fama da tsananin talauci da baƙar yunwa.
Har yanzu dai babu wani ingantaccen jawabi daga fadar shugaban ƙasar kan sayen jirgin, in banda hotunan jirgin da mataimakin shugaban kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar a shafukansa na sada zumunta
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI