Shugaba Tinubu ya fara yi wa ministocinsa garanbawul

Shugaba Tinubu ya fara yi wa ministocinsa garanbawul

Mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wannan Larabar.

 

Yanzu za a samu Ma'aikatar Raya Yankuna wadda za ta rika sanya ido kan ɗaukacin hukumomin raya yankuna kamar Hukumar Raya Yankin Niger Delta da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yammaci da kuma Hukumar Raya Kudu maso Yammaci da Hukumar Raya Arewa maso Gabashi- inji Onanuga.

Onanuga ya ƙara da cewa, Hukumar Wasanni ta Ƙasa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan Ma'aikatar Wasanni. 

Gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan matakin ne a yayin taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasar a wannan Larabar kamar yadda Onanuga ya yi ƙarin haske.

Kazalika shugaba Tinubu ya amince da matakin haɗe Ma'aikatar Yawon Buɗe Ido da Ma'aikatar Al'adu.

Kawo yanzu, babu wani cikakken bayani game da makomar tsohon Ministan Niger Delta, Abubakar Momoh da kuma tsohon Ministan Wasanni, John Enoh.

Kazalika babu cikakken bayani kan makomar Hannatu Musawa, domin ba a sani ba ko za ta ci gaba da jagorancin Ma'aikatar Al'adu ko kuma za a mika ragamar ce ga Lola Ade-John, wato Ministar Yawon Buɗe Ido.

Garambawul ɗin na zuwa ne a yayin da shugaba Tinubu ke shan matsin lamba don ganin ya aiwatar da matakin na sauye-sauye a majalisar ministocinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)