Shugaba Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa kan kisan Sarkin Gobir

Shugaba Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa kan kisan Sarkin Gobir

A cikin sanarwar da mai Magana da yawun shugaban Najeriya Ajuri Ngelele ya fitar, ya ce shugaban ya bayyana kisan basaraken a matsayin cin zarafi da kuma tozarci da bazai bari a cigaba da aikawa ba.

Ya kumayi ta’aziyya ga iyalan marigayin, da masarautar Gobir da ma gwamnatin Sokoto.

Ya kuma yiwa ‘yan Najeriya albishir da cewar gwamnatinsa a shirye take wajan yakin ayyukan ‘yan ta’addah.

shugaban ya bayyana cewar yana yin duk mai yuwuwa wajan ganin ya tabbatar da tsaro a kasar, sai 'yan siyasa da al'ummar kasar na cigaba da bayyana takaicin su gane da rashin tsaro da yafi kamari a yankin arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)