Wannan na zuwa yayin da aka samu zazzafar adawa tsakanin yan takara dake son lashe zaben na gobe.
Jamiyyun siyasa 17 ne za su fafata a wannan zabe to sai dai jamiyyu 3 na APC da PDP da LP ne hankula ya karkata kansu.
Sanata Monday Okpebholo ne ke wa jamiyyar APC takara ita kuwa PDP ta tsayar da Asue Ighodalo a matsayin dan takararta, ita kuwa LP ta tsayar da Olumide Akpata.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar mai magan ada yawun hukumar INEC a Najeriya ta tabbatarwa da RFI Hausa cewa tuni suka aike da kaya zuwa ƙananan hukumomin jihar Edo baki ɗaya kuam suna jiran gobe ne asabar don gudanar da zabe.
“An raba kayayyakin zabe waɗanda ba masu muhimmanci sosai ba tun satin da ya gabata, jiya Alhamis an raba masu muhimmanci sosai ɗin ta yadda kowacce ƙaramar hukuma a jihar Edo suka zo suka ɗauki kayan zabensu a babban bankin na ƙasa dake jihar Edo kamar yadda yake a al’ada suka tafi zuwa ƙananan hukumominsu”
Haj. Zainab Aminu ta bada tabbacin cewar hukumar zaben ƙasar INEC za ta yi zabe na adalci tare da miƙa nasara ga wanda alumma suka zabe.
“Ina amfani da wannan dama na sanar da al’ummar jihar Edo cewa kamar yadda shugaban hukumar zabe ya faɗa wanda suka zaba shi ne hukumar zabe za ta sanar a matsayin wanda ya lashe zaben”
Domin sauraron cikakkiyar tattaunawa da mai magana da yawun INEC a Najeriya Hajiya Zainab Aminu Abubakar, ku latsa wannan adireshi https://youtu.be/LbcYiqHQspU
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI