Wata tawaga da tsohon gwamnan ya jagoranta zuwa birnin Abeokuta ta ziyarci tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da tsohon ministan tsaon Theophilus Yakubu Danjuma domin tattaunawa da samun shawarwari a kan manufarsu.
Bayan kammala ziyarar a Lagos tsohon gwamnan Kano Malam Shekarau ya shaidawa RFI Hausa cewa babban dalilin da ya sa suka fara tintibar masu ruwa da tsaki shine, domin nemo masu tunanin samar da shugabanci na gari ba kawai a yankin arewacin Najeriya ba har ma da ƙasar baki ɗaya.
Shekarau ya ce a cikin tafiyar da suka fara suna son su zaburar da al’umma tun daga matakin mazaba har zuwa matakin ƙasa domin su gano waɗanda zasu yi musu adalci, kuma su tallata su a basu dama ta shugabanci a Najeriya.
“Ba mu ce mun fi kowa iyawa ba, amma mun yarda cewa a arewa da kuma ƙasar nan baki ɗaya muna da nagartatttun mutane da gogaggun waɗanda idan aka basu dama, zamu zaburar da al’umma domin su hango duk wanda suka san yana da wata gogewa da adalci da kuma gaskiyar da zai jagoranci mutane da adalci, domin mu yi yunkuri mu tallata su, mu fito da su a basu dama su zo su gabatar da abinda suke yi”.
“A yadda ake tafiya an mayar da siyasa ta zama ta kuɗi, ta zama ta ubangida, suna ɗorawa mutane shugabanci ko sun iya, ko ba su iya ba, ko sun dace, ko ba su dace ba, ko suna da ƙwarewa ko basu da ita, kuma duk yadda suka dama haka ake sha”.
Shekarau ya ce suna son su zaburar da ƴan ƙasa daga arewa dake da ƙuri’a mafi yawa da ma ƙasa baki ɗaya cewar su daina la’akari da abinda ake basu ranar zabe ta yadda wasu ke dasa shugabannin da basu cancanta ba.
Tsohon gwamnan na Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce za su nemi haɗin kan duk wanda yake son bada gudunmawa kuma zasu samu nasara.
Ya ce babban ƙudirinsu a ƙarshe shine a samar da shugabanci na gari a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI