Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta labarin nada mai rikon mukamin hafsan sojin kasa

Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta labarin nada mai rikon mukamin hafsan sojin kasa

Wannan na zuwa ne baya raɗe-raɗin cewa hafsan sojan ya rasa ransa a sakamakon cutar daji.

Wasu daga cikin kafafen yaɗa labarai na cikin gidan ƙasar ne suka fara ruwaito labarin cewa hafsan sojan ya rasa ransa a ƙasar waje, a sakamaon jinyar cutar kansa ko kuma daji, to sai dai tuni shalkwatar tsaron ta musanta labarin mutuwar, tana mai cewa tabbas jagoran na sojoji yana ƙasar waje karkashin kulawar likitoci amma yana nan da ransa.

Jim kaɗan bayan sanarwar da ta yi watsi da labarin mutuwar ne kuma, wata sabuwa ta sake ɓulla da ke cewa shalkwatar tsaron ta yi sabon naɗin rikon kwarya a mukamin na Laftanar Kanar Lagbaja.

Ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalwakatar tsaron, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce babu wani dalili dai zai sa a naɗa mai rikon kwarya a muƙamin na Laftanar Lagbaja, saboda kawai yaje a duba lafiyarsa a wani ɓangare na hutunsa na shekara.

Sanarwar ta ƙara da cewa dukannin ɓangarorin rundunonin tsaron Najeriya na ƙarƙashin kulawar ƙwararrun mutane don haka a yanzu babu wani dalili na sauya su ko kuma maye gurbinsu.

Tukur Gusau ta cikin sanarwar ya gargadi masu yaɗa irin wannan labari da su kuka da kansu matukar suka shiga hannun hukuma, yayinda kuma ya shawarci kafafen yaɗa labarai da su rika tantance labari daga mahukunta kafin yaɗawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)