SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu da muƙarrabansa su bayyana kadarorin da suka mallaka

SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu da muƙarrabansa su bayyana kadarorin da suka mallaka

Hakanan ƙungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da ya ƙarfafa mataimakainsa Kashim Shetima da minitocinsa da gwamnoni da kuma ‘yan majalisun ƙasar da suma su bi sahun a wannan shiri na ƙoƙarin bayyana alkiblarsu.

SERAP ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a yau ranar Lahadi mai kwanan wata 28 ga Disamba, 2024, wanda ke ɗauke sanya hanun mataimakin Darakta na SERAP, Kolawole Oluwadare.

Kungiyar ta yabawa Tinubu kan furucin da ya yi a kwanan baya a yayin tattaunawarsa ta farko a kafafen yada labarai na shugaban kasa, inda ya nuna cewa a shirye yake kotun ta CCB ta bayyana kadarorin da ya mallaka.

SERAP ta ce, "Yin hakan zai haifar da ɗa mai ido in har kuka buƙaci kotun ta CCB ta bayyana adadin dukiya da kadarorin da kuka mallaka da karfafawa Mataimakin Shugaban ƙasar da Ministoci da mambobin Majalisar Dokoki ta Kasa da Gwamnonin Jihohi da kuma shugabannin kananan hukumomi suka yi haka.”

A cewar Kungiyar, “hikimar bayyana kadarorin da manyan jami’an gwamnati suka gabatarwa wa CCB zai ci gaba da saukaka almundahana a dukkan matakan gwamnati, musamman a jihohi 36 na kasar, da babban birnin tarayya, da ma’aikatu da hukumomin tarayya MDAs, da kuma kananan hukumomi."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)