Saudiya zata daina bayar da biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashe 13

Saudiya zata daina bayar da biza ga ƴan Najeriya da wasu ƙasashe 13

Rahotanni sun ce wannan hukunci tuni ya fara aiki a wannan wata na Fabarairu inda ya shafi ƙasashen irin Najeriyar da Algeria sai Bangladesh da kuma Masar sannan Habasha da India da Indonesia da kuma Iraq da Jordan baya ga Morocco da Pakistan da kuma Sudan da Tunisia sannan Yemen.

Rahotanni sun ce Saudiya ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar Mahajjata marasa rijista a kusan dukkanin aikin hajji, lamarin da ke shafar walwalar da kulawar daya kamata mahajjatan su samu.

Miliyoyin Mahajjata ne daga ƙasashe daban-daban ke shiga Saudi Arabia don gudanar da ibadar ta Hajji kowacce shekara tsakanin watan Zul-Qida zuwa Zul-Hajji wadda ke matsayin guda cikin rukunan addinin musulunci.

Ko a bara mahukuntan Saudiyan sun yi barazanar kamewa da kuma tsare al’ummomin waɗannan ƙasashe 14 a gidan yari matuƙar aka kama su a wuraren ibada ba tare da izinin aikin na Hajji ba.

Wannan hukunci na nuna cewa al’ummomin waɗannan ƙasashe 14 daga yanzu baza su sake samun bizar shekara guda kamar yadda ake basu a baya don gudanar da harkokinsu na kasuwanci ko kuma ziyartar ahalinsu ba.

A cewar kamfanin tafiye-tafiye na TravelBiz, Saudi Arabia zata riƙa baiwa al’ummomin ƙasashen 14 ne bizar kwanaki 30 kuma idan ta ƙare babu zaɓin tsawaitawa face ficewa daga ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)