Satar allon kabari ya kai matsahi kurkuku a Kano

Satar allon kabari ya kai matsahi kurkuku a Kano

Kotun ta ba da umarnin yanke hukuncin kisa ƙeyar matashin zuwa kurkuku ne bayan da ya amsa laifin sace allunan kabari na ƙarfe guda 15 a makabartar.

Daga nan alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya yanke masa hukuncin daurin wata shida a gidan yari tare da umarnin yi masa bulala 30.

Tun da farko mai gabatar da ƙara  Insfekta Abdullahi Wada, ya shaida wa alƙalin cewa a ranar Talata ne aka kai ƙarar matashin a ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dala.

An kai ƙarar matashin ne da cewa ya shiga cikin maƙabarta ya sace allunan kabari shaida na karfe guda akalla 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)