Wannan naɗi ya biyo bayan irin gudumawar da Dakta Bedu wanda ya fito daga masarautar ke bayarwa ta fanni ci gaban yankin a bangaren ilimi.
Basaraken ya bayyana haka ne a karshen mako lokacin da ya karbi malamin jami'ar tare da wasu fitattun 'yan masarautar a fadarsa dake Fataskum.
Sarkin ya bukace shi da ya ci gaba da bada gudumawa kamar yadda yake yi wajen gina jama'ar masarautar ta fanni da ya kware na ilimi a matsayinsa na fitaccen malamin jami'a da ya fito daga yankin.
Dakta Bedu wanda ya yaba da karramar da aka masa ya kuma yi alkawarin ci gaba da taimakawa jama'ar masarautarsa da kuma jihar Yobe baki daya domin ganin an samu ci gaba a bangaren ilimi a fannoni daban daban.
Bedu ya taba zama wakilin RFI Hausa a Damaturu baya ga zama shugaban kungiyar 'yan jaridu ta jihar kafin ya koma jami'ar Suleyman Demirel dake kasar Turkiya inda ya samo digiri na 3 da ya kai shi matsayin Dakta.
Bayan dawowarsa gida, sai ya kama aiki a jami'ar Maiduguri inda yanzu haka yake aikin koyarwa da kuma bada gudumawa wajen ci gaban al'umma da kuma bincike ta fannin al'adu da kuma harsuna.
Bedu ya yi rubuce rubuce da dama a bangaren al'adu da kuma wallafe wallafe wadanda suka zarce 30 a manyan kafofi na kasa da kuma duniya baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI