Sanatocin Arewacin Najeriya sun buƙaci a gaggauta maido da wuta a yankin

Sanatocin Arewacin Najeriya sun buƙaci a gaggauta maido da wuta a yankin

A cikin wata sanarwar bayan taro da shugaban ƙungiyar Sanata Abdulaziz Yar’adua ya sanya wa hannu bayan taron da suka gudanar a yau Asabar a Abuja, sun buƙaci gwamnati ta gaggauta gyara layin wutar lantarki Shiroro zuwa Kaduna, wanda ke samar wa akasarin jihohin Arewacin Najeriya wuta.

Haka nan sun  ce akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan baiwa kayayyakin lantarkin Arewacin ƙasar kariya, don kare sake faruwar irin haka a nan gaba.

Kimanin mako guda ke nan ake fuskantar rashin wutar lantarki a yankin Arewacin Najeriya, sakamakon yadda batagari suka lalata wasu daga cikin turakun layin wutar lantarkin daya taso daga Shiroro zuwa Mando.

Wannan lamari dai ya shafi akasarin jihohin shiyar Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.

Tuni kamfanin da ke samar da wutar lankarki a Najeriya TCN ya ce ya gono inda matsalar ta ke, sai dai shugabar kamfanin Nafisatu Asabe Ali ta ce matsalar rashin tsaro ne ya hanasu gudanar da aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)