Sama da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin Maiduguri

Sama da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin Maiduguri

Ɗaya daga cikin jami'an da ke tsaren gidan yarin da ya buƙaci a sakaya sunansa, shi ne ya tabbatar wa da RFI Hausa cewa, fursunonin sun yi amfani da damar ibtila'in ambaliyar wajen tserewa.

Kazalika jami'in ya bayyana cewa, akwai mayaƙan Boko Haram da ake tsare da su a wannan gidan yarin na New Prison, kuma wasu daga cikinsu sun arce.

A ɓangare guda, akwai wasu fursunoni sama da 200 na daban da su kuma aka sauya musu gidan yari kamar yadda jami'in ya yi ƙarin haske.

Ambaliyar ta kuma rusa ɗakunan jami'an da ke tsaren gidan yarin.

Wannan na zuwa ne a yayin da al'ummar jihar Borno ke cikin zullumi biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye yankuna da dama a cikin tsakar dare.

Ya zuwa yanzu babu wani bayani a hukumance game da irin mummunar asarar da aka tafka a sakamakon ambaliyar ruwan wadda ta mamaye dubban gidaje da hanyoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)