Sama da ƴan Najeriya dubu 3 sun shiga aikin soji a Amurka tare da zama ƴan ƙasa

Sama da ƴan Najeriya dubu 3 sun shiga aikin soji a Amurka tare da zama ƴan ƙasa

Najeriya ce ta huɗu a jerin ƴan ƙasashen da Amurka ta ba su takardun zama ƴan ƙasa ta hanyar hidinmta mata a ɓangaren aikin soji tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024.

A jumulce, Amurka ta bai wa ƴan ƙasashen ƙetare kimanin dubu 52 takardun zama ƴan ƙasa a ƙarkashin aikinsu na soji a ƙasar.

Alkaluman da Hukumar Kula da Takardun Ƴan Ƙasa da Shige da Fice ta Amurka ta fitar a wannan Litinin, sun nuna cewa, ƴan asalin ƙasar Philippines dubu 5 da 630 ne suka samu takardun zama ƴan Amurka a ƙarƙashin aikin sojin, sai Jamaica da ke biye mata a matsayi na biyu, inda take da dubu 5 da 420, yayin da Mexico ke a matsayi na uku, inda take da dubu 3 da 670. Sai kuma Najeriya da ta zo ta biyar da adadin mutum dubu 3 da 270 da suka shiga aikin sojin tare da samun takardun zama ƴan Amurka.

Sauran ƙasashen sun haɗa da Ghana da Haiti da China da Kamaru da Vietnam da Koriya ta Kudu kamar yadda alkaluman hukumomin Amurka suka nuna.

Sojojin Amurka na ɗaura tutar ƙasar. Sojojin Amurka na ɗaura tutar ƙasar. AP

Alkaluman sun nuna cewa, adadin ƴan Najeriya da ke shiga aikin soji a Amurka na ci gaba da karuwa a kai a kai cikin shekaru biyar da suka gabata.

A shekarar 2020, ƴan Najeriyar 340 suka shiga aikin sojin na Amurka tare da samun takardun zama ƴan ƙasar, amma alkaluman sun haura zuwa 630 a 2021, kafin su sake ƙaruwa zuwa 680 a 2022, yayin da a bara, adadin ya kai 690, inda a bana alkaluman suka kai 930.

Bayanan da Amurka ta fitar sun nuna cewa, kusan rabin waɗanɗa suka samu wannan tagomashin na zama ƴan Amurka ƙarƙashin aikin sojin, shekarunsu na haihuwa na tsakanin 22 ne zuwa 30.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗimbin matasan Najeriya ke fafutukar neman shiga aikin soji a ƙasarsu ta asali, amma abin ya ci tura, yayin da ake zargin cewa, ƴan siyasa sun yi babakere wajen mamaye guraben da ake da su, inda suke bai wa wanda suka ga dama koda kuwa bai cancanta ba.

Masana harkokin tsaro sun ce, a halin da ake ciki, Najeriya na buƙatar ƙarin sojojin da za su ci gaba da yi mata yaƙi da ƴan ta'adda da ƴan bindiga da suka addadi sassan ƙasar, inda suke kashe-kashen bayin-Allah tare da sace dukiyoyinsu baya ga garkuwa da su domin karɓar kuɗin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)