Daya daga cikin 'yayan kungiyar kuma 'dan assalin jihar Barno, Dakta Aliyu Dala ya shaidawa RFI Hausa cewar sakamakon ambaliyar da ake yawan samu a yankin arewacin kasar sun gudanar da bincike na musamman a shekarar da ta gabata tare da bada shawara a kan hanyoyin da ya dace a bi wajen magance matsalar.
Ku latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Dakta Aliyu Dala
03:31
Hira tare da Dr.Aliyu Dala kan sakacin gwamnati game da ambaliyar Maiduguri
Dakta Dala wanda ke zama a Edinburgh ya ce daga cikin yankunan da bincike su ya gudana harda jihar Barno da kuma Madatsar ruwan Alo wanda fashewarsa ta kai ga jefa mazauna birnin Maiduguri cikin halin da suka samu kansu a yau.
Yadda ake gudanar da aikin agaji a Maiduguri AFP - AUDU MARTEMasanin ya ce da hukumomi sun yi amfani da shawarwarin da suka bayar, watakila da an kaucewa ganin irin illar da aka samu na asarar rayukan jama'a da gidaje da kuma kadarori.
Dakta Dala ya ce cikin shawarwarin da suka bai wa hukumomin harda bukatar samar da hanyar da ruwan dake madatsar Alo zai kwarara zuwa Tafkin Chadi idan aka samu karuwarsa da kuma bude shi ta hanyar da manoma zasu dinga noman rani.
Masanin ya ce akwai sakaci sosai na hukumomin da abin ya shafa, saboda haka kuskure ne a ce za'a jinginawa Ubangiji lamarin, alhali wasu mutanen da hakki ya rataya a kan su sun gaza wajen sauke alhakin da aka dora musu.
Dakta Dala ya bukaci daukar matakin ladabtarwa a kan duk wani jami'in gwamnati da aka samu da hannu wajen sakacin da aka gani.
Yadda ambaliyar ruwa ta tsananta a birnin Maiduguri. © dailytrustMasanin ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da kudaden da ake bukata domin aikin karkata akalar madatsar ruwan zuwa Tafkin Chadi domin kaucewa sake ganin irin wannan matsala ta bana.
Ya zuwa wannan lokaci babu wani adadi na hukuma dangane da yawan mutanen da suka mutu a ambaliyar, sai dai rahotanni na cewar sun zarce 100.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ke kasar China lokacin da aka gamu da iftila'in ya ziyarci birnin Maiduguri jiya litinin domin jajantawa jama'ar jihar dangane da wannan matsala.
Kafin zuwansa, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bada tallafi ga wadanda hadarin ya ritsa da su ciki harda motar shinkafa 50 domin rage musu radadin matsalar a ziyarar gani da ido da ya kai birnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI