Rundunar sojin najeriya ta tura sojojinta arewacin kasar domin baiwa manoma kariya

Rundunar sojin najeriya ta tura sojojinta arewacin kasar domin baiwa manoma kariya

A cewar babban ofishin tsaron Nijeriya, an tura sojojin ne domin samar da isasshen kariya da tsaro ga manoma daga ‘yan fashi da ‘yan ta’adda da sauran miyagun masu aikata laifuka a yankin.

Jibge sojojin zai taimaka wajen baiwa manoma da dama damar shiga gonakinsu, kamar yadda daraktar ayyuka da yada labarai na tsaro ta bayyana.

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta tabbatar da tura dakarun sojinta a yankin arewacin ƙasar, musamman a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar ƙasar.

Tura sojojin zai taimaka wajen bai wa manoma da dama damar shiga gonakinsu, kamar yadda daraktan hulda da jama'a na rundunar tsaro Manjo Janar Edward Buba ya bayyana wa manema labaru ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)