Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata kai harin kuskure kan fararen hula a Sokoto

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaryata kai harin kuskure kan fararen hula a Sokoto

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, wacce ke mai da martani game da rahotannin da ke cewar wani jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kai harin bam wasu kauyuka a ƙaramar hukumar Silame da ke jihar Sakoto, inda ake fargabar mutane da dama sun rasa ransu.

Rundunar ta ce sai da ta tabbatar da cewar inda ta kai harin a garuwan Gidan Sama da kuma Rumtuwa, suna da alaƙa da ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa.

Laftanar Kanar Abdullahi ya ce rundunar na gudanar da dukkan ayyukanta ne bayan tattara bayanan siri da kuma bincike.

Wasu majiyoyi sun ruwaito cewa mutane 10 ne suka rasu yayin hare-haren, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da faruwar harin, sai dai ya ce har yanzu suna aikin tantance irin ɓarnar da harin ya yi.

Tuni dai gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ziyarci kauyukan da abin ya faru don jajantawa iyalan waɗanda ibtila'in ya shafa, tare da yin alkawarin kafa kwamiti don gudanar da bincike akai.

Na kaɗu matuka da faruwan wannan lamarin, ba da gangan jami'an tsaro suka yi ba, haƙiƙa sun je kai wa ƴan ta'addan hari ne, sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda a hari na farko da na biyu, sai dai an samu kuskure a na uku.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun hare-heren kuskure kan fararen hula a Najeriya, wanda kuma ke haifar da asarar dimbin rayukan al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)