Rundunar sojin Najeriya ta amince da kisan fararen hula yayin zanga-zanga

Rundunar sojin Najeriya ta amince da kisan fararen hula yayin zanga-zanga

Wannan dai na zama wani sabon abu kan bayanin da rundunar ƴan sanda ta bayar na cewa ko mutum guda bai mutu sanadin harbin jami’an tsaro a yayin zanga-zangar ba.

To sai dai kuma duk da yadda rundunar ƴan sanda ta dage wajen musanta kisan fararen hula, an sami rahotanni da dama a sassan ƙasar da suka tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi amfani da ƙarfi wajen hallaka mutane.

An sami irin wannan rahoto a jihohin Niger, Kaduna, Jigawa, Borno, Katsina da kuma birnin tarayyar Abuja.

Shaidu da suka haɗar da faya-fayan bidiyo da hotuna sun tabbatar da faruwar wannan lamari, amma rundunar ƴan sandan ta yi ƙememe wajen amincewa da haka.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam, irin su Amnesty International sun yi Allah wadai da wannan lamari, inda suka buƙaci hukumomi su gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda aka samu da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)