
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babban sufeto Janar na ƴansandan ƙasar ya nemi afuwar kwamitin bin diddigi na Majalisar, a kan rashin amsa gayyatar da ya yi masa a baya, domin ya yi bayani a kan rahoton ofishin mai binciken.
A ranar talata ƴan Majalisar su ka bayyana rashin gamsuwa da bayanan da rundunar ƴan sandan ƙasar ta bayar a kan batun ɓacewar makaman daga mabanbantan ofisoshinsu da ke fadin ƙasar, inda su ka ce dole ta yi amansu.
A cewar kakakin babban mai binciken kudi na ƙasar Olu Samuel Godwin, rahoton binciken na shekarar 2019 ya nuna cewa a watan disamban shekarar 2018 kawai akalla bindigogi 178,459 ne suka ɓace.
Rahoton ya ƙara da cewa daga cikin makaman da suka yi ɓatan dabo akwai bindigogi kirar AK-47 guda 88,078. Baya ga haka rahoton ya kuma ce akwai batutuwan da su ka ci karo da juna daga cikin bayanan da rundunar ta gabatar.
Toh saidai daga cikin bindigogi 3,907 da su ka ɓace daga shekarar 1998 kawo yanzu, waɗanda ake tuhumar rundunar ƴan sandan Najeriyar a kai, guda 15 kacal ta iya ba da bayani a kan su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI