Rundunar ƴansandan Najeriya ta ƙaryata zargin ɓatar bingigunta kusan dubu 4

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ƙaryata zargin ɓatar bingigunta kusan dubu 4

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a yau Alhamis, ya ce zargin ya samo asali ne daga rahoton da ofishin babban mai binciken ƙudi na ƙasar ya gudanar daga tsakanin shekarar 2019, amma sai dai ya ce bai fayyace haƙiƙanin makaman da suka ɓace ba.

Ga dukkan alamu rahoton ya samo asali ne daga binciken da aka yi a shekarar 2019, mai yiwuwa bayanan da aka tattara sun zo ne kafin fara wa’adin Sifeto Janar na yanzu. Rahoton ya nuna cewa makamai dubu 3 da ɗari 907 ne  ba a san inda suka shigeba, ba ɓacewa aka ce sun yi ba, kamar yadda ake yadawa.

Wannan ƙarin haske da rundunar tayi dai ya biyo bayan wani rahoto ofishin mai bincike ƙudi na ƙasar ya miƙa wa kwamitin kula da harkokin jama’a na majalisar dattawar ƙasar, wanda ya yi ƙorafi game da saɓanin alƙaluman yawan makaman rundunar da aka samu.

A lokacin sauraron ƙorafin, kwamitin majalisar dattawan Najeriya ya nuna damuwa kan yadda bindigogi dubu 178 da ɗari 459 ciki har da ƙirar AK-47 dubu 88 da 78, aka yi zargin sun ɓace daga ofisoshin ƴansanda a faɗin ƙasar.

To amma a sanarwar da rundunar ta fitar a yau, ta ce alkaluma ba su wakilci asalin bindigun da rundunar ke da su a rumbun aje makamanta ba, domin ta yiwuwa lokacin binciken wasu bindigogin an fita aiki da su.

Ya kuma ce wasu daga cikin bindigogin sun ɓace ne a yayin wasu hare-haren da aka kai wa ƴansanda a lokacin da suke gudanar da aiki.

Kwamitin na majalisar dattawan Najeriya ya ɗage zamansa kan ƙorafin har zuwa ranar Litinin 17 ga watan Fabrairu nan, don bai wa rundunar ƴansandan ƙasar damar gabatar da bayanan alkaluman da aka samu saɓani a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)