Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama manyan masu laifuka sama da dubu 30 a 2024

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama manyan masu laifuka sama da dubu 30 a 2024

Babbban sufeton ƴan sandan na Najeriya Egbetokun ya ce sun ceto mutum dubu 1 da 581 da aka yi garkuwa da su a shekarar 2024.

Ya faɗi haka lokacin da yake jawabi a wani taron tattaunawa da manyan jami’an ƴan sandan ƙasar a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya ƙasar da cewa a shekarar ta 2024 sun samu nasarar ƙwato bindigogi dubu 1 da 984 da kuma kwato harsashi dubu 23 da 250

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ya fitar ya zayyana irin nasarorin da rundunar ta samu a shekarar 2024 yayin da suke shirin domin tunkarar shekarar 2025.

Babbban sufeton ƴan sandan na Najeriya Egbetokun ya yabawa dukkani jami’an rundunar bisa sadaukarwa da aiki tuƙuru da suke yi musamman wurin tabbatar da ganin an samu raguwar aikata laifuka a sassan Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)