Rahotanni sun ce mahaƙan na tsaka da aikin haƙar zinare ne ginin mahaƙar ya rufta suna ciki, wanda ya sanya tsammanin yiwuwar dukkaninsu sun rasa rayukansu musamman lura da lokacin da aka ɗauka gabanin kai ɗauki garesu.
Wani mai aikin haƙo da ibtila’in bai rutsa da shi ba, Adamu Jamtare ya ce galibin mahaƙan sun fito ne daga ƙaramar hukumar Gashaka kuma kawo yanzu ba a iya nasarar ɗakko su daga ruftawar da gini ya yi suna ciki ba.
Bayanai sun ce mutanen su 22 na aiki ne haramtacciyar mahaƙar wadda ke gandun dajin gwamnati na Gashaka-Gumji da ya haɗa yankunan ƙananan hukumomin Gashaka da Toungo a jihohin Taraba da Adamawa inda ya rutsa da su baki ɗaya ba tare da tsiran ko mutum guda ba.
Shugaban ƙaramar hukumar Toungo Injiniya Suleiman Toungo ya bayyana nasarar iyta ɗakko gawarwakin mutane 5 amma ya ce ba shi da tabbas game da yawan waɗanda suke ƙarƙashin ƙasa.
A cewar Inijiniya Suleiman lamarin ya faru kusan wata guda da ya gabata, kuma ya ƙunshi ƙananun yara daga jihohi da dama.
Yankin wanda aka yi ittofaƙin ya na ɗauke da tarin albarkatun ƙarƙashin ƙasa kusan kowacce shekara ana ganin mutuwar ɗaruruwan mutane da ke zuwa aikin haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba.
Wasu rahotanni sun ce ko a bara fiye da mutum 70 sun rasa rayukansu a makamancin wajen a ƙoƙarinsu na haƙar zinare.
Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar ta Taraba ta tabbatar da faruwar ibtila’in.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI