
Rahotanni sun ce wasu daga cikin waɗannan Ƴansanda da umarnin ya shafa, sun ce ba zasu aje kakinsu ba muddin shugabansu, wato Sufeto Janar Kayode Egbetokun ya ki tuɓe nasa kakin, lura da cewar tun a shekarar da ta gabata ya cika shekaru 60 a duniya, kuma bisa ƙa'idar dokar aikin gwamnatin Nijeriya, ya dace ace ya yi ritaya kamar waɗanda suka gabace shi.
Tuni Hukumar kula da aikin 'Yansanda ta kasa a ƙarƙashin jagorancin Hashimu Argungu, tsohon muƙaddashin Sufeto Janar mai ritaya, ta bada umarni ga Sufeto Janar cewar duk jami'in Ɗansandan da ya cika shekaru 35 yana aiki, ko kuma ya cika shekaru 60 da haihuwa, ya dace ya tafi ritaya.
Bayanai da dama sun ce Sufeto Janar Egbetokun ya ki aiwatar da wannan umarni, abinda ya sa wasu daga cikin wadanda wannan umarni ya shafa suke ci gaba da zama a ofisoshinsu.
Wasu bayanai sun ce wasu daga cikin wadanda umarnin ya shafa kai tsaye sun ruga kotu domin ƙalubalantar Hukumar kula da aikin Ƴansandan wadda ta nemi su aje kakin su saboda cimma wa'adin aikin su ta fuskar shekarun aiki ko kuma na haihuwa.
Wasu daga cikin wadanda suka yi magana da Jaridar Daily Trust sun bayyana dalilin kin ritayar ta su da ci gaba da zaman Egbetokun wanda suka ce ya ki ritaya bayan cika shekaru 60, yayin da kuma dokar aikin Ƴandan ta yi bayani karara akan hakan.
Sai dai wasu bayanai kuma na cewa gwamnati mai ci na amfani ne da sabuwar dokar ta Majalisar Dattawa ta amince da ita, wadda ta ce ta mayar da ofishin Sufeto Janar mai wa'adin shekaru 4.
Wasu bayanai na daban sun ce yanzu haka Sufeto Janar Egbetokun ya kafa wani kwamiti domin zakulo sunayen waɗanda suka cika shekaru 60 da haihuwa kuma suka ki ritaya domin ladabtar da su, yayin da wasu ke dangata matakin da zuwa kotu da wasu daga cikin su suka yi domin ƙalubalantar ci gaba da zamansa a ofis.
A makon gobe ne ake saran kotun ta fara sauraron ƙarar da wasu daga cikin manyan jami'an Ƴansanda suka shigar domin ƙalubalantar umarnin cewar su tafi ritaya daga aiki.
Tuni ƙungiyoyin fararen hula irin su CISLAC ta hannun shugabanta Awwal Musa Rafsanjani suka bukaci mutunta dokar aikin gwamnatin Nijeriya a tsakanin jami'an Ƴansandan dake aiki.
Bisa ƙa'idar aikin Ƴansanda, Hukumar dake kula da aikin da ake kira PSC ne ke da hurumin ɗaukar jami'ai da kara musu girma da kuma ladabtar da duk wanda aka samu ya aikata laifi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI