Rikicin makiyaya da manona yayi sanadiyyar asarar rayuka a jihar Adamawa

Rikicin makiyaya da manona yayi sanadiyyar asarar rayuka a jihar Adamawa

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar  SP Suleiman Nguroje ya bayyana cewa, an tura tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa domin dawo da zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa sai dai ya ce har yanzu ba a kama wani mutum ba.

 

A iya cewa rikicin  ya zama ruwan dare a yankin, domin ana yawan samun arasar rayuka da dama da kuma asarar dukiyoyi na miliyoyin nairori.

Rahotanni sun ce rikicin baya-bayan nan ya samo asali ne sakamakon kisan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wani matashi a garin Kodomun, lamarin da ya haifar da tashe-tashen hankula a yankunan da ke kewaye.

Dangane dangane da batun ne sarkin sarkin yankin,Homun Alhamdu, Hama Batta, da shugaban karamar hukumar Demsa, Akham Jalo, suka kira wani taron gaggawa, wanda suka  bukaci masu ruwa da tsaki da su nemi a kawo karshen rikicin.

 

Yayin taron sun yanke shawarar cewa zasu nemi gwamatin jihar  ta ba makiyaya umarnin  kwashe shanunsu a lokacin noma da damina,haka zalika an umurci shugabannin kungiyoyin da ke yaki da rikicin da su gano tare da kai rahoton wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su gaban kuliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)