Rikici ya tilasta wa fiye da mutum miliyan 1 barin matsugunansu a Najeriya - NBS

Rikici ya tilasta wa fiye da mutum miliyan 1 barin matsugunansu a Najeriya - NBS

A cewar NBS fiye da kashi 63 na yaran da ke cikin wannan adadi na ƴan gudun hijira basa samun damar karatu yayin da suke tsananin buƙatar agaji kama daga abinci, tufafi da sauran abubuwan buƙata.

Rahoton da NBS ta fitar ta ce kashi 77 na yawan ƴan gudun hijirar na tsananin buƙatar komawa ga gidajensu sakamakon tsawon lokacin da suka ɗauka a matsugunan wucin gadi.

NBS ta sanya jihar Borno a matsayin wadda ke da yawan ƴan gudun hijira sakamakon ayyukan Boko Haram da kuma ibtila’in ambaliyar ruwa na baya-bayan nan da jihar ta gani.

Alƙaluman da NBS ta fitar a jiya Litinin ya nuna cewa jihar Borno kaɗai na da ƴan gudun hijira dubu 206 da 753 daga cikin jumullar ayarin gida guda ko kuma magidanta dubu 251 da dubu 82 da ake da su a Najeriya baki ɗaya.

Binciken da hukumar ƙididdigar ta Najeriya ta gudanar ya nuna cewa kashi 83.4 na ƴan gudun hijirar sun shafe shekaru 4 zuwa sama a sansanonin wucin gadi yayin da wasu kashi 12.4 suka shafe shekaru 2 zuwa 3 a sansanonin, ko da ya ke akwai wasu kashi 0.2 da suka shiga sansanin wucin gadin a kwanakin baya-bayan nan.

Alƙaluman na NBS sun ce jihohin  Adamawa da Yobe, da Borno baya ga Sokoto da Katsina da kuma Benue da Nasarawa su ne kan gaba a yawan mutanen da rikici ya raba da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)