Wannan na ƙunshe a wata wasika da gwamnatin Rasha ta aikewa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya wadda jaridar Dailytrust ta samu ta hannun sakataran watsa labaran ofishin jakadancin Rasha na Najeriya Yury Paramonov.
Ana zargin ƙasar Rasha da hannu kan dambarwar siyasa a ƙasashen Mali da Burkin Faso da Nijar.
A Najeriya kuwa a baya-bayannan aka ga yadda jami’an tsaron ƙasar suka kama wasu masu zanga-zanga saboda ɗaga tutar Rasha, inda rundunar soji a ƙasar ta ce hakan tamkar laifin cin amanar ƙasa ne.
Wannan lamari ya janyo damuwa kan ko akwai sa hannun wasu daga ƙasashen waje kan zanga-zangar dake faruwa a Najeriya.
To sai dai ƙasar Rasha ta zargi Amurka da Birtaniya da Ukraine cewar suna alaƙantata da zanga-zanga domin lalata kyakykyawar alaƙarta da Najeriya. Inda ta shawarci gwamnatin ƙasar ta yi watsi da alaƙantasu da ake yi da zanga-zangar.
“Bayanan da sakataran harkokin wajen Amurka Antony Blinken da tsohon daraktan ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya David Robert da Ambasadan Ukraine a Najeriya Ivan Kholostenko su ka yi, babu kunya kuma ba tare da wata hujja ba na cewar ɗaga tutocin Rasha lokacin zanga-zanga a Najeriya na nuna yadda ƙasar ke da hannu kan wannan lamari tare da yin gargaɗin cewar hakan zai ci gaba da faruwa”.
“Ofishin jakadancin Rasha na amfani da wannan dama domin fitowa ƙarara ya yi watsi da duk waɗannan zarge-zarge, tare da jaddada cewar Rasha ba ta da hannu kan zanga-zangar da ta faru a Najeriya ko kuma wadda ake tunanin za ta faru a nan gaba”.
“Ko yaushe Rasha na mutunta kasancewar Najeriya ƙasa mai cin gashin ƙanta”.
Sakataran ofishin jakadancin na Rasha a Najeriya Yury Paramonov ya kuma miƙa saƙon taya murna daga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zuwa ga shugaban Najeriya Bola Tinubu kan zagayowar ranar samun ƴancin kan Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI