Oyo: mutane da dama sun mutu yayin turmutsitsi a wani bikin nuna al'adu

Oyo: mutane da dama sun mutu yayin turmutsitsi a wani bikin nuna al'adu

Duk da cewa ba’a bayyana yawan adadin mutane da suka rasa rayukansu ba, amma gwamnatin Oya ta ce galibi ƙananan yara ne.

Turmutsutsun ya faru ne a wurin taron al’adu da aka shiryawa ƙananan yara a wata makarantar mai suna Basorun High School da ke Ibadan, lamarin da ya haddasa asarar rayuka, baya ga wasu da dama da suka samu raunuka a yau Laraba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, ministan yaɗa labarai na jihar, Prince Dotun Oyelade ya ce an kai mutanen da abun ya shafa zuwa asibitoci mafi kusa a Ibadan domin basu kulawar gaggawa.

Ya ce ba su da labarin cewa za’a gudanar da taron kwata-kwata, hasali ma da sun bayar da gudunmawa ta kowace fuska domin gudanar da bikin na ƙarshen shekara da aka shiryawa ƙananan yaran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)