A jawabin da ya yi a yayin taron shugabanci na Chinua Achebe, da ya gudana a Jami’ar Yale da ke Amurka, Obasanjo ya kuma buɓaci ganin an rage tsawon wa’adin shugabannin hukumar ta INEC, da kuma ɗaukar kwararan matakai wajen naɗasu ta hanyar kaucewa baiwa waɗanda ke da ra’ayin wata jam’iya matsayi.
Dole ne Najeriya ta tabbatar da naɗin sabbin shugabannin INEC masu gaskiya a matakin ƙasa da jiha da kuma ƙananan hukumomi, tare da rage tsawon wa’adisu don dakatar da tasirin siyasa da cin hanci da rashawa, da kuma sake dawo da yarda ga tsarin zaɓe a wajen al’umma.
Obasanjo ya kuma yi nuni da yadda hukumar ta gaza yin amfani da fasahar zamani musamman na’urar BVAS da kuma ta IreV da ake amfani da ita wajen bayyana sakamakon zaɓe, a lokacin zaben shugaban ƙasar na shekarar 2023, duk kuwa da alkawuran yin hakan da shugaban hukumar ya yi.
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce wannan matsalar da aka samu a lokacin, ta taimaka matuka wajen tabka kura-kurai da dama a zaɓen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI