
Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano Hashimu Dungurawa ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai yau litinin a jihar.
Sauran ƴan majalisar da aka dakatar sun haɗa da Ali Madakin Gini mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala da Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da kuma Sani Rogo da ke wakiltar ƙananan hukumomin Rogo da ƙaraye a majalisar dokokin Najeriya.
NNPP ta zargi ƴan majalisun da ta dakatar da saba ƙa’ida da kuma dokokinta.
Dakatarwar da NNPP ta yi wa waɗannan ƴan majalisa na zuwa kwana guda bayan da shugaban jam'iyyar APC a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa akwai waɗanda ke shirin komawa APC daga NNPP.
A baya-bayannan ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci bikin yaye ɗalibai a jami’arsa inda ak ga fuskokin jiga-jigan APC kamar shugabanta na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Barau Jibril.
Jam’iyyar ta ce ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan abin da ya faru domin kamo bakin zaren, sannan kuma NNPP ta ce ƙofa a buɗe take domin tattaunawa dukda dakatar da waɗannan ƴan majalisu da ta yi.
To sai dai jam'iyyar NNPP ta ce idan waɗanda aka dakatar suka nemi afuwa to ƙofa a bude take domin duba yiwuwar basu dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI