NNPCL ya gayyaci Obasanjo don ganin yadda matatun man ƙasar suka fara aiki

A wata sanarwa da jami’in hulaɗa da jama’a na kamfanin Olufemi Soneye ya fitar, ta ce NNPCL ya ɗauki matakin ne don Obasanjon ya je ya tabbatar da yadda ake gudanar da aikin tace mai a matatar da ke jihar Rivers.

Muna mika goron gayyatar ga tsohon shugaban ƙasa Obasanjo da ya ziyarci matatun mai da aka kamma gyaransu, ya kuma shaida irin ci gaban da aka samu.

Wannan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban ƙasar Obasanjo a gidan Talabijin na Channels, inda ya ƙalubalanci aikin da aka ce matatar na yi.

A cewar jami’in hulda da jama’a na NNPCL Olufemi Soneye, ba wai kawai gyara don tada matatun suka yi ba, sun kuma tabbatar da cewar an sauya fasalinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)