Babban mai kula da harkokin kudaden kamfanin Umar Aliyu ya ce an samu karin abinda ya kai naira biliyan 700 akan ribar da ya samu a shekarar 2022, wanda shi ne kashi 28 na kudaden da suka samu.
Taron NNPC da manema labarai © NNPCAliyu ya ce sun samu nasarar ce sakamakon jajircewar su wajen inganta ayyukan da suke yi duk da matsaloli daban daban da suke fuskanta.
Jami'in ya danganta wannan ci gaba da suka samu da sabuwar dokar man ta kasa wadda ta mayar da kamfanin ya zama na kasuwanci mai dauke da hannayen jarin hukuma da kuma jama'a.
Aliyu ya ce nan gaba kadan zasu bayyana shirin sayar da hannayen jarinsu da zaran an gudanar da taron wadanda ke rike da jarin kamfanin da kuma hukumar gudanarwarsa.
Jami'in ya kuma bayyana aniyarsu ta ganin sun kara yawan man da Najeriya ta ke hakowa kowacce rana zuwa ganga miliyan 2 nan da karshen wannan shekara ta 2024.
Dangane da dogon layukan man da ake ganin a birnin Lagos da Abuja, mataimakin shugaban dake kula da bangaren man Dapo Segun ya ce suna hada kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an warware matsalar da ake fuskanta domin ganin an wadata jama'a da man.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI