Shugaban NLC Joe Ajaero wanda ya bayyana matuƙar kaɗuwa da ƙarin farashin na mai ya ce gwamnatin Najeriyar ta karya alƙawari yayinda ta saje jefa jama’ar ƙasar a matsananciyar wahala.
A cewar shugaban na NLC tun farko sun janye daga matakinsu na neman naira dubu 250 a matsayin mafi ƙarancin albashi ne saboda yadda gwamnati ta sha alwashin ɗaukar dukkanin matakan da suka dace waɗanda za su hana tashin farashin man fetur.
Comrade Ajearo ya bayyana cewa sanin gwamnatin Najeriya ne cewa ƙarin farashin da ta yi kan man fetur zai sake jefa ma’aikata a gagarumar matsala lura da cewa naira dubu 70 ba za su ishesu tafiyar da rayuwarsu a wata guda ba.
Bisa ga yarjejeniyar da NLC ta cimma da gwamnatin ta Najeriya, ƙungiyar ƙwadagon za ta haƙura da naira dubu 70 ne kaɗai bisa sharaɗin ba za a ƙara farashin man fetur ba, amma matuƙar farashin ya tashi zuwa naira dubu 1 da 500 ko dubu 2 ko shakka babu kai tsaye ƙungiyar za ta nemi naira dubu 250 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikta.
Wannan mataki na gwamnatin Najeriya game da ƙarin farashin man na zuwa ne wata guda bayan ƙulla yarjejeniyarta da NLC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI