A lokacin da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ke gana wa da manema labarai a Abuja a cikin daren jiya, ya ce sun dakatar da yajin aikin ne don ba da damar ci gaba da tattaunawar da su ke yi da gwamnati.
Ya ce gwamnati ta amince ta kafa kwamiti mai ƙarfi, da zai kunshi wakilai biyar-biyar daga ɓangarensu da kuma na gwamnati, don yin bitar tsarin kuɗin kiran waya a ƙasar, sannan ya gabatar da rahotansa a cikin makwanni biyu.
Ita dai hukumar ta NCC ta ce ta amince da da ƙarin kuɗin kiran wayar ne sakamakon faɗuwar darajar kuɗin naira da hauhawan farashin makamashi da dai sauransu da aka samu a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce matakin na ta, ya yi dai-dai da dokar hukumar ta shekarar 2003, sai dai ƙungiyar kwadago ta Najeriya ta ce hakan zai sa ke jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI