Ministan Ilimin na Nijeriya ya ce za a hukunta duk wani jam'in Nijeriya da aka samu da hannu wajen amincewa da shaidar digirin ta boge.
A yayin da Gwamnatin Nijeriya ta ce ta bankaɗo shaidar digiri ta bogi guda 22,739 daga wasu jami'o'i a Jamhuriyar Benin da Togo.
Ministan ya bayyana wannan nasara ce ya a ranar Juma'a a Abuja, yayin wani taron manema labarai.
Farfesa Tahir ya ce,
“daga bayanan da ke hannun Hukumar Masu Yi wa Ƙasa Hidima NYSC, an gano cewa akwai "ɗalibai 21,634 da suka gabatar da shaidar digiri ta bogi wacce suka samo daga Benin daga 2019 zuwa 2023. Sannan mun kuma gano shaidar digiri ta bogi 1,105 daga Togo," in ji ministan.
Kana Majalisar Zartarwa ta ƙasa ta amince a kori waɗanda aka gano sun gabatar da shaidar karatu ta bogi daga ƙasashen, waɗanda suke aiki a ma'aikatun gwamnatin tarayya.
A yayin da bayyana cewa mutanen sun gabatar da shaidar digiri ce daga jami'o'in da ƙasashen ba su amince da su ba.
Farfesa Tahir Mamman ya kuma yi karin haske a kan cewa duk ɗalibin da ya gabatar da shaidar digiri daga jami'o'in da ake koyarwa da Turancin Ingilishi na Faransanci ba daga shekarar 2017, to sakamakon bogi ya gabatar.
Ministan ya bayyana cewa duk ma’aikatan da aka samu da hannu cikin wannan badaƙala, to tabbas zasu fuskanci matakan ladabtarwa. Sannan sassan da ke kula da aikin, su ma ana yi musu garambawul.
Matakin na gwamnati ya biyo bayan wani bincike da wani ɗan jarida ya yi, inda ya ce ya samu shaidar digiri daga wata jami'a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida, ba kuma tare da ya halarci koda darasi daya ne jami'ar ba.
A watan Disambar 2023 ne, ɗan jaridar na Daily Nigerian, Umar Audu, wanda ya yi basaja a matsayin ɗalibi ya nuna shaidar digiri na bogi da ya samo daga Benin har ma kuma ya shiga sansanin Masu Yi wa Ƙasa Hidima a Naijeria da wannan sakamakon, bayan ya samu sahalewar ma'aikatar ilimi.
Lamarinin da ya ɗauki hankali sosai a Nijeriya a wancan lokacin, har ma gwamnati ta ce ta ɗauki mataki don magance matsalar, wacce ake gani ta samu karɓuwa ne saboda haɗin bakin wasu jam'ian gwamnatin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI