
Da wannan mataki ɗai, masu amfani da ƙananan motoci za su rinƙa biyan harajin naira ɗari biyar a kowace madakatar toll gate, su kuma masu manyan motoci su rinƙa biyan 1,600, sai dai motocin jami’an tsaro abin bai shafe su ba.
Gwamnatin Nijeriya dai ta samar da madakatar toll gate har huɗu a Keffi da Akwanga da Lafia sai kuma Makurdi a kan hanyar da ke da nisan kilo mita 227.2.
A lokacin da ya ke ƙaddamar da toll gate ɗin, ministan ayyuka na Nijeriya David Umahi, ya ce ta hanyar amsar kuɗi a toll gate, gwamnati za ta samu damar inganta hanyoyinta a duk faɗin ƙasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken rahoton Khamis Saleh...........
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI