Nijeriya: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda fiye da 70 a jihar Borno

Nijeriya: Sojoji sun kashe ƴan ta’adda fiye da 70 a jihar Borno

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikataar tsaron ƙasar, Manjo Janar  Markus Kangye ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar.

Kangye ya ce dakarun sun gano wasu injinan jirgi biyu a wani wuri da jiragen suka fadi da daɗewa a jihar Borno, kana suka amso manyan bindigogi 104 da harsasai dubu 2,639.

Har ila yau Daraktan ya kuma ce dakarun sun kama wasu barayin mai 36 tare da kwace man da darajarshi ya haura miliyan 646.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikataar tsaron ƙasar, ya lissafa wasu daga cikin kayayakin da aka sata a yankin Neja Delta waɗanda dakarunsa suka yi nasarar kwato su. Sun haɗa da ɗanyen mai lita dubu 497,152 da lita dubu 142,000 na iskar gas, sannan lita dubu 4,075 na man fetur.

Baya ga wadannan kayakin da su ka kwace, sun kuma lalata na’urorin tace danyen mai 164, da jiragen ruwa 19, da tankuna 16, akwai kuma randunan adana 38, da ma wurare akalla 42 da ake gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)