Nigeria: NNPCL ya ce matatar Ɗangote ya gaza samar da yawan fetur da ake buƙata

Nigeria: NNPCL ya ce matatar Ɗangote ya gaza samar da yawan fetur da ake buƙata

Wannan lamari ne ma ya sa ake ganin kamfanin da dillalan mai za su koma shigar da mai daga ƙasashen waje kamar yadda harkar ta ke kafin yanzu.

Amma a wani martani da ya  mayar, babban jami’in yaɗa labarai da rukunin kamfanonin Ɗangote, Anthony Chiejina ya musanta ikirarin na NNPCL, yana mai bayyana shi a matsayin ƙarya tsagwaronta.

An sa ran matatar Ɗangote ta samar da litar man fetur har miliyan 25 duk rana a watan Satumba, kana a watan Oktoba ta samar da lita miliyan 30 duk rana, kuma  a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba aka fara jigilar man daga matatar  Ɗangote.

Sai dai kakakin kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye ya ce lita miliyan 10 da dubu ɗari 3 ne kawai aka samu daga matatar, saboda haka kamfanin zai nemi hanyar  cike giɓin da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)