Obasanjo wanda ke mayar da martani a kan iƙirarin Janar Gowon dangane da rubuta wasiƙar ya ce da ya san da haka da yaje ya gode masa lokacin da ya fita daga gidan yari.
Olusegun Obasanjo ya ce bayan sakinsa ya ziyarci mutane da dama a ciki da wajen Najeriya yana musu godiya akan gudunmawar da suka bayar wajen kuƙutar da shi, amma bai je wurin Janar Gowon ba saboda ba shi da labari a kai, sai jiya da ya yi maganar.
Saboda haka Obasanjo ya godewa tsohon mai gidan na sa da kuma duk waɗanda suka bada gudunmawa wajen ceto rayuwarsa daga hannun Abacha.
Gowon da Obasanjo sun yi waɗannan kalamai ne a wajen bikin addu'oin Kirismeti da gwamnatin jihar Filato ta shirya.
Obasanjo da Murtala ne dai suka kifar da gwamnatin Janar Gowon a shekarar 1975.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI