
Kame riƙaƙƙun masu safarar ƙwayoyin na zuwa a dai dai lokacin da hukumar ta NDLEA ta kuma yi nasarar kame wasu miyagun ƙwayoyi na Colorado da Loud da kuma Tramadol a jihohin Kano da Kogi bayan da masu safarar suka ɗurasu a tukunyar gas da aka shigo dasu daga ƙasar daga Canada.
Rahotanni sun ce guda cikin riƙaƙƙun ƴan safarar ta miyagun ƙwayoyi da aka bayyana sunansa da nyekwonike Elochuckwu Sylvanus mai shekaru 30, na da fasfo biyu da ya ƙunshi guda na Najeriya da wannan suna, sai kuma wani na Saliyo da sunan Kargbo Mohamed Foday.
A cewar hukumar ta kame Elochuckwu ne a ranar 2 ga watan da muke na Fabarairu a filin jirgin saman Fatakwal lokacin da ake tantance fasinjan da suka sauka daga jirgin Qatar Air da ya taso daga Doha ya yada zango a Abuja gabanin isowa jihar.
NDLEA ta ce an yi amfani da nau'ra mai gani har hanji, wadda ta gano ƙwayoyin da basu narke a cikinsa ba, dalilin da ya tilasta kwankwaɗa masa magungunan da suka tilastashi fitar da ƙulli 62 na hodar ta iblis mai nauyin kilogiram 1 da ɗigo 348.
Bayanai sun ce Onyekwonike Elochuckwu Sylvanus da yake amfani da sunan Kargbo Mohamed Foday ya yi ƙaurin suna wajen safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasashen Thailand da Pakistan da kuma Iran baya ga ƙasashen yammacin Afrika.
Ɗan safarar miyagun ƙwayoyin na biyu da NDLEA ta bayyana sunanshi da James Herbert Chinoso mai shekaru 48, an kame shi ne a filin jirgin saman Lagos ranar 1 ga watan Fabarairu kuma ya sauka ne daga jirgin Ethiopian Air bayan da ya yo nashi balaguron daga Madagascar ya ratsa Addis Ababa zuwa Najeriya.
Hukumar ta ce ta yi amfani da na’urar mai gani har hanji ne gabanin gano kwantattun ƙwayoyi a cikinsa da basu narke ba, kuma bayan fitar da su ne aka samu ɗauri 63 na hodar iblis mai nauyin gram 909.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI