Jami’in yaɗa labarun hukumar ta NAPTIP Vincent Adekoye ne ya bayyana nasara da jami’ansu suka samu ga manema labaru a yayin da yake gabatar musu da jawabi.
Adekoye ya ƙara da cewa an sami wurin ne a cikin wani rukunin gidaje a yankin Ushafa dake ƙaramar hukumar Bwari dake Abuja babban birnin tarayyar ƙasar, a yayin da ya ke cewa sun mamayi wannan wuri ne bayan wasu bayanai da suka samu daga wasu masu kishin ƙasa.
Ya ce an samu waɗannan mutane ne a kulle a cikin wani gida a sanadiyar ɗaya daga cikin waɗanda suka killace matan da ba’a fayyace shi ba, bayan da aka ɗaukesu aikin na aika-aikar da suka nema ta wani shafinsu na yanar gizo.
Adekoye ya kuma ce, Darakta-Janar ta Hukumar, Hajiya Binta Adamu-Bello, ta yabawa bangaren shari’a, bisa gagarumin hukuncin da aka yanke na yankewa wani Bishop Kenneth Duke hukunci.
An dai ce Duke ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade, wacce diya ce ta ɗaya daga cikin mabiya cocinsa a Abuja.
Shugabar ta ce wannan hukuncin na iya zama izna ga ire-iren masu irin wannan aika-aikar, yayin da ta yi gargadin cewa hukumar ba za ta kyale duk wanda ya karya dokarta ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI