Nan da kwanki uku wutar za a maido da lantaki za Arewacin Nijeriya - Adelabu

Ministan ya bayyana hakan ne alokacin da ya ke amsa tambayoyin daga sanatocin ƙasar, lokacin da suka gayyace shi a jiya Talata kan rashin wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

Sama da kwanaki goma ke nan da babu lantarki a Arewacin ƙasar, sakamakon yadda ƴan ta’adda suka lalata wasu daga cikin kayayyakin layin wutar daya tashi daga Shiroro zuwa Kaduna, wanda kuma shi ke samar da akasarin wutar da ake amfani da ita a yankin.

A cewar shugabar hukumar samar da wutar lantarkin ƙasar Nafisatu Ali, sun tanaji dukkanin kayan da ake buƙata don gyaran, sai dai ta ce matsalar tsaro ba zai basu damar zuwa wajen ba.

A martanin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya yi, ya umarci hukumomin tsaro su tabbatar da sun samar da tsaron da ake buƙata don gudanar da aikin gyaran.

Daga cikin matakan gaggawa da hukumomin Najeriya ke ɗauka don maido da lantarki yankin Arewacin ƙasar, ministan ya ce suna ƙoƙarin fara samarwa jihohin yankin da abin ya shafa lantarki daga tasharsu ta Ugwuaji zuwa Makurdi.

Za a dawo da wuta a Arewa nan da kwana biyu zuwa uku masu zuwa. Za mu yi amfani da layin na Ugwuaji zuwa Makurdi don wannan aikin na wucin gadi.

Ya kuma ƙara da cewa, ana nan ana ci gaba da ƙoƙarin samar da tsaro  don gyara layin wutar da ƴan ta’adda suka lalata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)