Nan bada daɗewa ba Lakurawa za ta zama tarihi - Janar Oluyede

Nan bada daɗewa ba Lakurawa za ta zama tarihi - Janar Oluyede

A lokacin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a fadar shugaban ƙasar da ke Abuja bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu, ya ce suna nan suna ƙoƙarin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaron a faɗin ƙasar.

Hafsan sojojin ƙasa na Najeriya wanda a kwanakin nan ya ziyarci wasu sansanonin sojin ƙasar, ya bayyana kwarin gwiwa kan yadda Najeriya ke ci gaba da haɗa kai da ƙasashen da ke makwabtaka da ita domin yaƙar ta’addanci.

Muna yaƙarsu a Najeriya, kuma da zarar mun fatattakesu a nan, sai su matsa zuwa Jamhuriyar Nijar. Yanzu da Jamhuriyar Nijar ta shiga cikin yaƙin, hakan na nufin nan ba da jimawa ba, Lakurawa za ta zama tarihi.

Game da ziyarar da ya kaiwa shugaban ƙasar kuwa, ya ce ya baiwa shugabaTinubu tabbacin cewa zayyi iya ƙoƙarinsa wajen inganta lamuran tsaro a ƙasar.

Najeriya dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke yammacin Afrika da ke fama da matsalar tsaro, musamman mayaƙan Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabashi da ta ƴan bindiga a shiyar Arewa maso Yammaci sai ta tsagaren Niger Delta a kudancin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)